2019: An fada mani idan na koma APC, za a yafe mani – Obadiah Mailafia

2019: An fada mani idan na koma APC, za a yafe mani – Obadiah Mailafia

‘Dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya a zaben 2019, Obadiah Mailafia, ya bayyana yadda APC ta nemi ya dawo cikin tafiyar jam’iyyar saboda a yafe masa zunubansa.

A Ranar Talata, 17 ga Watan Satumban 2019, Obadiah Mailafia yake cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi kokarin janyo sa a jikin ta da nufin za a yafe masa laifin da bai taba aikatawa a Duniya ba.

A cewarsa, Jiga-jigan APC sun yi tunanin ya na harin shigowa jam’iyyar ne bayan zabe. Mailafia ya yi wannan bayani ne lokacin da ya zanta da Menama labarai a Hedikwatar ADC a Garin Abuja.

Obadiah Mailafia wanda ya taba rike kujerar mataimakin gwamnan babban bankin CBN ya ce:

“A gabanin zabe, an matsa mani lamba, inda aka rika mani tambayoyi game da abubuwan da su ka faru a CBN kusan shekaru goma da su ka wuce, abubuwan da ba a sashe na ma su ka faru ba.”

KU KARANTA: Dakarun Najeriya sun zagaye harabar gidan Jaridar Sahara Reporters

“Aka nemi a kitsa mani sharri da cewa idan na shiga APC, za a yafe mani. Na fada masu cewa meyasa su ba za su dawo jam’iyya ta ba. Har na tambaye su me zai hana Buhari dawowa ADC?”

“Me ya ke da shi da ba ni da wanda ya fi sa? Na ce mutanen su ‘yan zamanin da ne za su ceci Najeriya? Mutumin da bai taba amfani da kyamfuta ba. Me za su kara iya yi wa Najeriya?”

A game da shari’ar P & ID, tsohon ‘dan takarar ya ja-kunnen gwamnati da ta bi sannu a hankali ka da ta jefa kasar cikin babban rikici inda yace manyan Duniya ne su ka kitsawa kasar kutungwila.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel