Yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin wani dan majalisar wakilai da abokansa su 3

Yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin wani dan majalisar wakilai da abokansa su 3

Yan bindiga sun yi garkuwa da Mista Robert Igali, wani hadimin dan majalisar wakilai mai wakiltan kudancin Ijaw a jihar Bayelsa, Mista Preye Oseke.

An tattaro cewa yyan bindigan sun yi garkuwa da Igali tare da abokansa guda uku a hanyar garin Elele da ke karamar hukumar Emohua na jihar Rivers.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka sacen na a hanyarsu ta komawa Yenagoa daga wajen bikin aure na Oseke a jihar Imo lokacin da lamarin ya afku a karshen mako.

Masu garkuwan sun far masu ne a kusa da garin Elele sannan suka dauke su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Igali ya kasance Shugaban ma’aikatan tsohon shuggaban kungiyar matasan Ijaw kuma kwamishinan matasan jihar Bayelsa mai ci, Mista Udengs Eradiri.

Wata majiya tace masu garkuwan sun tuntubi iyalansa a Igali sannan sun nemi a biya fansar naira miliyan 5 kafin su sake shi da abokansa.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An kama Aisha Zakari matar da take kiran gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu tana tsorata shi ta wayar salula

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ke da nasaba da garkuwa da yaran Shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Matazu da ke jihar, Kabiru Matazu guda biyu.

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya sanar da kamun a hedkwatar rundunar da ke Katsina a ranar Talata, 18 ga watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel