Albashi mafi karanci: Za mu iya fara yakin aiki kowane lokaci - Kungiyoyin Kwadago

Albashi mafi karanci: Za mu iya fara yakin aiki kowane lokaci - Kungiyoyin Kwadago

- Kungiyoyin kwadago sun yi kira ga 'yan Najeriya su gargadi gwamnati gwamnatin tarayy kan aiwatar da albashi mafi karanci

- Kungiyoyin sun ce dukkan tattaunawar da su kayi da gwamnati kan albashi mafi karancin ya ci tura

- Kungiyoyin kwadagon sun gargadi gwamnati cewa akwai yiwuwar za su shiga yajin aiki na gama gari muddin ba kaddamar da albashi mafi karancin ba

Hadakan kungiyoyin ma'aikata da ke tattaunawa kan batun karin albashi sun bukaci 'yan Najeriya su fadawa gwamnatin tarayya da kaddamar da sabon albashi mafi karanci domin kare afkuwar yakin aiki.

Hadakar kungiyoyin ma'aikatan karkashin jagorancin Trade Union ne tayi wannan kirar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

Mukadashin shugaban kungiyar, Mista Achaver Simon da sakataren kungiyar Mista Alade Lawal sun ce yunkurin gwa kungiyoyin ma'aikatan su kayi na tursasa wa gwamnati ta kaddamar da albashi mafi karancin ya ci tura.

Sun ce kungiyoyin ma'aikatan sun bawa gwamnati isashen lokaci domin biyan bukatun ma'aikatan amma bisa ga dukkan alamu gwamnati ba za ta yi abinda ya dace ba har sai an gudanar da yajin aiki.

Ya ce kungiyoyin ma'aikatan ba za su sake yi wa gwamnati gargadi ba kafin ma'aikata da ke jihohin Najeriya za su fara yajin aiki nan rashin aiwatar da albashi mafi karanci da sauran gyare-gyare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel