Na samu sha tara na arziki daga wajen yan kungiyar IPOB a Amurka – Ministan Buhari

Na samu sha tara na arziki daga wajen yan kungiyar IPOB a Amurka – Ministan Buhari

Ministan kwadago a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Chris Ngige ya bayyana cewa yayan kungiyar tawaye masu rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB sun yi masa sha tara na arziki a yayin ziyarar daya kai kasar Amurka a kwanakin baya.

Rahoton jaridar Sahara ta bayyana cewa Ngige ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da shuwagabannin kabilar Ibo a garin Obosi na jahar Anambra, inda yace IPOB ta karramashi, saboda shima ya basu kulawa a yayin da yake gwamnan Anambra.

KU KARANTA; N30,000: Za mu iya shiga yajin aiki kowanni lokaci daga yanzu – ma’aikatan Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ngige ya yi kira ga kafatanin kabilar Ibo da su daina kallon kansu a matsayin saniyar ware a siyasar Najeriya, sa’annan ya shawarcesu da su shiga dumu dumu a fafata dasu a siyasar Najeriya.

“Ku dai ihun ana nuna muku wariya bayan baku shiga an dama daku ba, ku tashi tsaye a yi gwagwarmaya daku, Najeriya ta mu ce duka, adalci shine a bar kabilar Ibo ta samar da shugaban kasa a 2023, amma fa sai mun yi aiki tukuru zamu samu.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yana son a samu shugaban kasa daga Ibo, don haka dolene mu bashi goyon baya, mu shiga APC, babu wanda zai baka shugaban kasa kana cikin dakinka.” Inji shi.

Idan a'a tuna a kwanakin baya ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya ci dukan tsiya a hannun yan kungiyar IPOB a kasar Jamus inda ya je halartar taro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel