Rusau a Kaduna: Yan kasuwannin Kaduna sun fara yi ma El-Rufai addu’a

Rusau a Kaduna: Yan kasuwannin Kaduna sun fara yi ma El-Rufai addu’a

Yan kasuwan jahar Kaduna sun fara gudanar da addu’o’i na musamman a kan gwamnatin jahar Kaduna sakamakon manufar gwamnan jahar Kaduna na rusa wasu manyan kasuwannin jahar tare da sake ginasu ginin zamani.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito yan kasuwan sun bayyana rashin gamsuwarsu da manufar gwamnatin na zamanantar da kasuwanni, musamman duba da cewa bata basu wani wurin da za su cigaba da gudanar da kasuwancinsu ba.

KU KARANTA: N30,000: Za mu iya shiga yajin aiki kowanni lokaci daga yanzu – ma’aikatan Najeriya

A cikin wata hira da aka yi da gwamnan jahar Kaduna, gwamnan ya tabbatar da burinsa na fadada wasu kasuwannin jahar tare da zamanantar dasu, da suka hada da Kasuwar barci, kasuwar sabon gari da kuma babbar kasuwar Kaduna na Sheikh Gumi.

“Kasuwannin nan suna bukatar a fadadasu, kuma zamu fadadasu, kuma zamu gina sabbin kasuwanni na zamani a unguwanni inda mutane zasu iya kama hayan shaguna, daga nan zamu wuce Zaria da Kafanchan don gina sabbin kasuwanni, dole ne kawai mu gyara Kaduna.” Inji shi.

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya kara da cewa zasu gina sabbin kasuwanni a garin Rigasa na karamar hukumar Igabi, da kuma garin Zonkwa.

Sai dai wasu daga cikin yan kasuwan sun bayyana damuwarsu game da wannan aiki, musamman yan kasuwan barci, wanda suka ce sun fara addu’ar kada Allah Ya baiwa gwamnan ikon aiwatar da wannan manufa.

Wani Tela dake kasuwar barci, Sani Muhammad ya bayyana cewa: “Muna fara addu’o’i na musamman a kan wannan manufa, saboda yawancinmu muna cikin damuwa game da aikin, saboda zamu rasa abin yi idan aka fara aikin.”

Shi ma wani mai suna Jafaru Madobi yace: “Wannan zalunci ne, saboda a yanzu haka duk mun dimauce, mun sani idan aka rusa kasuwan ba zamu sake samun shago ba, mu jari muke so daga wajen gwamnan ba aikin fadada kasuwa ba.

Haka zalika wani dan gwanjo mai suna Usman Mani yace: “Mun shiga damuwa tun bayan maganan da gwamnan ya yi saboda bamu da na yi, me yake su mu yi, tun da yawancin bamu da kudin da zamu iya kama shago? Kuma bamu ji ya yi maganan biyan kudin fansan shagunan da zai rusa ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel