Fayose da EFCC: Ranar 21 ga Oktoba Alkali zai cigaba da shari’a

Fayose da EFCC: Ranar 21 ga Oktoba Alkali zai cigaba da shari’a

Rahotanni na zuwa mana cewa shari’ar da ake yi da tsohon gwamman jihar Ekiti, Aydole Fayose, za ta cigaba a Ranar 21 ga Watan Oktoban 2019. Ana shari’ar ne a babban kotun tarayya an Legas.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta na zargin Ayodele Peter Fayose da wawurar kudi Naira billiyan 6.9 daga asusun jihar Ekiti a lokacin yana gwamna.

A Oktoban bara watau 2018 ne hukumar EFCC ta fara gurfanar da Mista Ayodele Peter Fayose a gaban Alkali mai shari’a Mojisola Olatotegun na babban kotun tarayya da ke zama a Garin Legas.

Hukumar ta jefi tsohon gwamnan na PDP da laifuffuka 11 wanda su ka hada da sata da wawurar kudi. Daga baya an sake gurfanar da tsohon gwamnan a gaban Chukwujekwu Aneke a cikin 2019.

Fayose ya karyata zargin da ke wuyansa inda hakan ya sa aka nemi a bada belinsa da sunan zai tafi asibiti a kasar waje domin a duba lafiyarsa. Kotu ta lamunce masa hakan, amma da sharadi.

KU KARANTA: Fayose ya yi wa Kayode Fayemi raddi kan batun bashin Ma'aikata

Sharadin da aka ba tsohon gwamnan kasar kafin a bada belinsa a kan kudi Naira miliyan 50 shi ne za a kawo fasfonsa gaban kuliya a Ranar 16 ga Satumban nan ko kuma kafin wannan lokaci.

Daga nan ne Alkali mai shari’a C. Aneke ya dakatar da zaman kotu har sai zuwa 16, da 17 da 18 da kuma 19 ga Satumba, inda za a fara zaman shari’a zuwa 21, 22, 23, 24 da 25 na Watan Oktoba.

Hakan na nufin a Ranar 21 ga watan gobe za a sake komawa kotu da Ayo Fayose domin kotu ta na hutu a wannan lokaci a dalilin wani bita da ake yi wa manyan Alkalan Najeriya a halin yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel