Akwai sauran 'yan Najeriya 817 a Afirka Ta Kudu da ke jiran a kwasu su - FG

Akwai sauran 'yan Najeriya 817 a Afirka Ta Kudu da ke jiran a kwasu su - FG

- Babban wakilin Najeriya a kasar Afirka ta kudu, Godwin Adama, yace babu kasa da 'yan Najeriya 817 da ke jiran dawowa gida

- Yawan mutanen da suka yi rijistar dawowa gida ya karu zuwa 1,004

- Tuni dai an shawo kan matsalar da ta hana jirgin Najeriya sauka a kasar Afirka ta kudu a jiya

A ranar Laraban makon da ya gabata, gwamnatin tarayya ta kwaso 'yan Najeriya 187 daga kasar Afirka sakamakon harin da 'yan kasar ke kaiwa baki.

A jiya Talata, babban wakilin Najeriya a kasar Afirka ta kudu, Godwin Adama, a tattaunawar waya ya sanar da wakilin jaridar Punch cewa yawan mutanen da zasu dawo Najeriya ya karu zuwa 1,004.

A satin da ya gabata, gwamnatin tarayya tace mutane 604 ne suka yi rijistar dawowa gida Najeriya.

A jiya Talata, mutane 320 ne jirgin Air Peace ya shirya kwasowa amma an samu tsaiko sakamakon rashin yarjewar gwamnatin kasar akan saukar jirgin.

Kwaso 'yan Najeriya 150 a makon da ya gabata ya samu tsaikon sa'o'i 15 wanda kasar Afirka ta kudun ta jawo.

Samun mutane 1,004 da suka yi rijistar dawowa gida tare da cire mutane 187 na wadanda suka dawo a makon da ya gabata, zamu iya cewa akwai akalla mutane 817 da ke jiran a kwaso su zuwa gida Najeriya.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra

Babban wakilin Najeriya a kasar Afirka ta kudu ya sanar da jaridar Punch cewa 'yan Najeriya 320 ne za a kwaso a yau Laraba.

Kamar yadda ya ce, tuni an shawo kan matsalar da ta kawo tsaiko tun farko.

Ya yi koken cewa wasu daga cikin wadanda suka yi rijistar basu bayyana a filin jirgin ba, hakan baya baiwa jami'an kwarin guiwa.

Adama ya kara da bayyana cewa wadanda basu da fasfo din Najeriya ana basu shaidar tafiya ta gaggawa ne, wanda yace tuni an shawo kan ire-iren matsalolin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel