Masu garkuwa da mutane sun sace babban lauyan Najeriya

Masu garkuwa da mutane sun sace babban lauyan Najeriya

- Masu garkuwa da mutane sun sace babban lauyan Najeriya, Chike Onyemenan a jihar Delta

- Tuni dai suka tuntubi iyalansa don karbar kudin fansa har naira miliyan 15

- Wasu masu garkuwa da mutanen sun afkawa yankin Uvwiamuge inda suka yi awon gaba da mutane babu adadi

Masu garkuwa da mutane sun kama babban lauyan Najeriya, Chike Onyemenam, a babban titin Benin zuwa Asaba kusa da Meta City housing estate, Issle-Azagba, jihar Delta.

Southern City News ta gano cewa anyi garkuwa da lauyan ne a ranar Litinin tare da wadanda suka rakasa duba wata kadararsa a babban titin.

Wani daga cikin iyalansa ya ce masu garkuwar sun saki sauran inda suka canzawa lauyan wuri.

Wata majiya ta ce masu garkuwar sun kira iyalansa tare da bukatar naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra

Hakazalika, bata gari kusan 20 an samu rahoton sun fada yankin Uvwiamuge na Ughelli/Agbarho na sashin titin gabas maso yamma a karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba.

Abin ya auku wajen karfe 6:30 na yammacin ranar Litinin wanda ya dau kusan mintuna 30.

Ganau ba jiyau ba sun ce, bata garin sun tsere ne bayan da suka yi musayar wuta da jami'an 'yan sandan da suka iso wajen.

Majiya da dama sun ce masu garkuwar da mutanen sun kwashe kusan mutane 8 ne don garkuwa da su.

Wata majiyar kuma ta ce mutane 4 masu garkuwar suka sace suka yi cikin daji dasu.

Masu ababen hawa da suka nufi Ughelli da Effurun sun tsere tare da barin ababen hawansu don gudun fadawa tarkon miyagun.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adeyinka Adeleke, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin Ughelli, ya yi ikirarin bai san anyi garkuwa da babban lauyan ba.

Adeleke ya sanarwa manema labarai cewa mutum daya kacal aka yi garkuwa da shi a Ughelli, ya kara da, "Bansan anyi garkuwa da babban lauyan ba a Asaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel