Ba zan biye maka ba, ka biya Ma’aikata hakkin su – Fayose ga Fayemi

Ba zan biye maka ba, ka biya Ma’aikata hakkin su – Fayose ga Fayemi

Kwanan nan ne gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiri ya fito ya na kokawa da cewa gwamnatin da ya gada ta Ayodele Fayose ta bar masa dinbin bashin kudin sallamar ma’aikata na Biliyan 57.

Ayodele Fayose wanda ya mulki jihar daga 2014 zuwa 2018, ya yi wuf ya yi wa gwamnatin APC mai-ci raddi inda yace ba zai biyewa gwamna Fayemi su tsaya har su na wani dogon surutu ba.

Fayose ya ce: “Ba tare da wani mamaki ba, na karanta abin da (Kayode) Fayemi ya ke fada kamar yadda ya saba na wasa da adadin kudin da ma’aikatan jihar Ekiti su ka bi gwamnati na bashi.”

Tsohon gwamnan ya kuma ce: “Ba tare da na biye masa ba, maimakon in fito in fitar da jawabi, zan yi kira gare shi ya biya ma’aikatan kudinsu. Dama can an zabe shi ne ya yi abin da na gaza.”

Tsohon gwamnan ya kara da cewa: “Mai girma Kayode Fayemi, ina taya ka murna yayin da ka cika shekaru guda a ofis, ina sa rai ka yi ayyukan da jama’a za su gani, domin da su za a tuna ka,"

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dauki shawarar Abokin hamayyarsa bayan ya ci zabe

A karshe tsohon gwamnan na jam’iyyar PDP ya fadawa Magajin na sa, Fayemi, ta Tuwita cewa shi kam ba zai sake yin takarar gwamna ba don haka ya nemi su zauna lafiya ba tare da rikici ba.

Ayo Peter Fayose ya yi mulkinsa na farko ne shekaru 15 da su ka wuce inda ya sake dawowa gado a 2014, ya kuma kammala wa’adinsa a bara amma ya gaza daura wanda zai gajesa gwamna.

Fayemi ya na kukan cewa gwamnatin PDP ta bar masa tarin bashin kudin sallamar ma’aikata na Biliyan 57 wanda Ayo Fayose ya ki biya a lokacinsa. Tsohon gwamnan bai musanya zargin ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel