N30,000: Za mu iya shiga yajin aiki kowanni lokaci daga yanzu – ma’aikatan Najeriya

N30,000: Za mu iya shiga yajin aiki kowanni lokaci daga yanzu – ma’aikatan Najeriya

Hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta bayyana cewa a shirye take ta fantsama yajin aiki a kan rashin biyan karancin albashin naira dubu 30 da gwamnati ta yi, don haka yan Najeriya ma su zauna cikin shiri, in ji kungiyar.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamitin kungiyar kwadago dake tattaunawa da gwamnatin tarayya game da tsare tsaren aiwatar da fara biyan karancin albashin ne ta bayyana haka a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, inda ta yi kira ga yan Najeriya su roki gwamnati ta yi abinda ya kamata kafin ta dauki mataki.

KU KARANTA: Yadda wata budurwa ta burma ma Saurayinta wuka, ta kashe shi har lahira

Shugaban kwamitin, Simon Anchaver da sakatarensa Alade Lawal ne suka fitar da wannan sanarwa a babban birnin tarayya Abuja, inda suka ce sun baiwa gwamnati isashshen lokacin duba bukatun ma’aikata tare da biyan bukatain, amma alamu sun nuna gwamnati bata da burin cikawa.

Don haka kwamitin ta ce ba za ta sake gargadin gwamnati game da wannan batu ba, sai dai kawai uwar kungiyar kwadago ta umarci ma’aikatan Najeriya su fara yajin aiki irin na sai baba ta ji a kan wannan batu na rashin biyan karancin albashin N30,000.

A wani labara, ita ma kungiyar malaman kwalejojin ilimi na Najeriya, COEASU, sun yi ma gwamnatin Najeriya barazana fadawa yajin aiki na dindindin matukar ba ta amince da bukatunsu ba.

Kungiyar ta yi wannan barazana ne sakamakon yin watsi da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da gwamnatin tarayya game da wasu muhimman bukatunta da ta mika ma gwamnati gabanin janyewar wancan yajin aiki da ta yi.

Shugaban kungiyar, Nuhu Ogirima tare da sakataren kungiyar, Taiwo Olayanju ne suka rattafa hannu a kan sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Talata, 17 ga watan Satumba bayan kammala taron kungiyar da aka daga ranar 10 zuwa 11 ga wata a Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel