Moghalu ya yabawa Buhari a kan nada Majalisa mai kula da tattalin arziki

Moghalu ya yabawa Buhari a kan nada Majalisa mai kula da tattalin arziki

A cikin makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani kwamiti ko majalisar musamman da za ta rika ba shi shawara game da harkokin da su ka shafi tattalin arziki.

Wannan mataki da shugaban kasar ya dauka ta jawo masa yabo daga Masana tattalin arziki a kasar musamman ganin yadda shugaba Buhari ya ajiye banbancin ra’ayin siyasa ya jawo Masana.

Farfesa Kingsley Moghalu shi ne wanda ya sake fitowa ya yabawa gwamnatin shugaba Buhari a kan kafa wannan majalisar mashawartar. Moghalu ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita.

Moghalu wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2019 ya bayyana cewa tun farko ya ba da irin wannan shawara a littafin nan na sa da ya rubuta mai suna Build, Innovate and Grow (BIG).

Farfesan ya ke cewa a cikin shafi na 273 ya kawo wannan magana na cewa a kafa majalisar masana tattali da za su rika ba shugaban kasa shawarar inda gwamnatinsa za ta sa gaba.

KU KARANTA: Attajirin Duniya Bill Gates ya yi magana game da Najeriya

Babban Masanin tattalin arzikin yake cewa akwai bukatar shugaban wannan majalisa mai dauke da mutane kamar 5 ko 6 ya zama babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattali.

A cikin wannan littafi da Moghalu ya rubuta domin ayyana manufofin da yake da shi ga Najeriya, yace ya kamata ‘yan wannan kwamiti su kware a bangaren kasuwanci, haraji, tattali, kudi, dsr.

‘Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar YPP ya na ganin zai yi kyau Ministoci su zama ba su cikin wannan majalisa, sai dai su dabbaka manufofin da mashawartar su ka ba shugaban kasa.

Haka dai aka yi, inda Gwamnati ta nemo kwararru a harkar tattali wanda ba su cikin Ministoci domin su rika bada shawara. Tsohon Gwamnan CBN Sanusi Lamido Sanusi ya yabawa wannan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel