A karshe NECO za ta saki sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 yayinda gwamnatin Neja ta biya N200m

A karshe NECO za ta saki sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 yayinda gwamnatin Neja ta biya N200m

Gwamnatin jihar Neja tace ta biya hukumar jarrabawar NECO naira miliyan 200, domin tabbatar da ganin an saki sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 wanda hukumar ta rike.

A wani jawabin daga Misi Mary Barje, Babbar Sakataren sadarwa ta Gwamna Abubakar Bello ta bayyana a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, cewa kudin ya kasance wani bangare na kudin jarrabawar da hukumar ke bin jihar.

Ta bayyana cewa gwamnatin ta biya fiye da naira biliyan daya zuwa ga hukumomin jarrabawa daban-daban cikin shekaru uku da suka gabata, duk cikin kokarin samar da ilimin boko kyauta ga dalibai a jihar.

Jawabin ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince zata biya hukumar jarrabawan naira miliyan 50 a kowani wata, don sauke bashin dake kasa.

Tace “Gwamnatin ta sadu da jami’an NECO; mun yi yarjejeniya, bayan mun biya wasu kudade cikin makon da ya gabata, hukumar tayi alkawatin sake sakamakon daliban.”

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi da makami a Lagas

Jawabin ya bayyana jajircewar gwamnatin da kuma kokarinta wajen bunkasa fannin ilimi, inda ta kara da cewa fannin yana da muhimmanci kwarai da gaske a gwamnatin da Bello ke jagora.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel