A Arewa: Wata mata ta kashe sabon jaririn kishiyarta

A Arewa: Wata mata ta kashe sabon jaririn kishiyarta

Hukumar yan sandan jihar Neja sun damke wata matar aure mai suna, Harela Uba, a kauyen Shakona, karamar hukumar Shiroro ta jihar kan kisan sabon jaririn kwana uku da haihuwa.

Kwamishanan yan sandan jihar, Alhaji Adamu Usman, ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da manema labarai a ranar Talata, 17 ga watan Disamba, 2019.

Usman ya bayyana cewa wani mutum mai suna Uba Saidu dan kauyen Shakodona a karamar hukumar Shiroro ya kai kara ofishin yan sanda cewa amaryarsa ta ajiye sabon jaririnta cikin daki yayinda ta shiga ban daki.

Dawowarta ke da wuya, sai ta ga wani kumfa-kumfa na fitowa daga bakin jaririn kuma da wuri aka garzaya da shi asibitin Kuta inda ya mutu daga baya.

KU KARANTA: Yaro ya dabawa mahaifinsa wuka har lahira a jihar Kano

Hukumar yan sandan ta gayyaci uwargidarsa mai suna, Harela Uba, domin amsa wasu tambayoyi saboda ita kadai ke gida lokacin da abin ya faru.

Bayan gudanar da bincike, ta tabbatar da cewa lallai ta baiwa diyarta mai shekaru bakwai, Khadija Uba, piya-piya domin durawa jaririn.

Ya ce za'a gurfanar da ita a kotu bayan kammala bincike.

A wani labarin daban, Wani matashi mai suna Habibu Ibrahim ya caccakawa mahaifinsa mai sune Malam Ibrahim Salihu mai shekaru 80 wuka har lahira a kauyen Asada, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Amma a ranar Talata, jami'an yan sanda sun bayyana cewa sun damke Habibu bayan ya arce daga garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel