Fatan da nake yi wa Najeriya - Bill Gates

Fatan da nake yi wa Najeriya - Bill Gates

Babban attajirin duniya kuma shugaban gidauniyar 'Bill and Melinda', Bill Gates, ya yi wata hira ta wayar tarho da 'yan jarida daga Najeriya, Stockholm, Uganda da sauransu inda ya yi magana a kan batutuwa da dama da suka shafi Najeriya.

A cewar Gates, "Najeriya kasa ce mai muhimmanci a wurina, tana daga cikin kasashen da gidauniya ta keda Ofis. Mun yi aiyuka da dama a Najeriya a kan rigakafin shan inna kuma mun koyi abubuwa da dama. An shafe kusan shekaru uku ba a samu mai cutar shan inna ba a Najeriya.

"Za mu cigaba da kokari wajen ganin mun kori cutar shan inna daga Najeriya gaba daya, amma abun da muka bawa fifiko yanzu shine inganta harkar lafiya a matakin farko a Najeriya.

"Idan ina da wani fata da nake wa Najeriya, bai wuce na ga kasar ta zuba isassun kudi a bangaren kiwon lafiya ba. Abu ne mai yiwuwa, saboda kasashe da basu kai Najeriya arziki ba sun yi hakan, kuma bangaren kiwon lafiyarsu ya inganta.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da nadin hadimai guda biyu da zasu yi aiki tare da Lai Mohammed

"Mu na hada gwuiwa da Aliko Dangote a yawancin aiyukan da muke yi a Najeriya, yana taimaka mana wajen fahimtar irin mutanen da za mu hada kai da su da kuma sadu wa da sarakunan gargajiya da zasu taimaka wajen ganin jama'a sun karbi abin da muka zo da shi.

"Najeriya na da matukar muhimmanci, ina kyautata wa kasar zato," a cewar Gates.

Attajirin ya bayyana cewa babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta shine; kudaden shigowa da gwamnati ke samu sun yi matukar kadan idan aka kwatanta da sauran kasashe.

Gates ya ce kasashe da dama dake irin matsayin Najeriya sun samu karuwar kudaden shigo wa da kaso 15% amma har yanzu Najeriya tana mataki na kasa da kusan kaso 6% kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel