Yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi da makami a Lagas

Yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi da makami a Lagas

Wata tawagar jami'a tsaro karkashin jagorancin shugaban yan sanda na reshen Igando, CSP Taiwo Kasumu, sun yi nasarar kama wasu manyan yan fashi da makami guda uku.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga kakakin yan sandan jihar Lagas, DSP Bala Elkana a ranar Talata, 17 ga watan Satumba.

"Yan fashin sun addabi mutanen yankin Igando/Egan da ke makwabtaka musamman a cikin dare."

"Sun isa unguwan ne a kan babura uku tae da niyar yin fashi a hanyar Ikotun-Igando amma sai yan sanda suka dakile yunkurinsu," inji Elkana.

Ya bayyana cewa an kama wani mai suna Oseni Waheed, dan shekara 32 da bindiga a inda lamarin ya faru yayin da sauran yan fashin suka tsere.

Elkana ya bayyana cewa har ila yau a saka su cikin jerin wadanda hukumar biciken masu laifi na jiha (CID) Yaba ke farauta bisa laififfukan da suka shafi fashi da makami da kuma kisan kai.

Ya bayyana cewa ana farautan su ne bisa kisan wani dan sanda dake karkashin reshen Amukoko a lokacin da suke gudanar da ayyukansu na fashi da makami.

KU KARANTA KUMA: Gyara: Buhari ya bukaci hukumar PSC ta daidaita sahun rundunar 'yan sandan Najeriya

Elkana har ila yau ya bayyana cewa yan sanda daga reshen Ilemba Hausa ta kama yan fashi biyu, Mista Gidion Amuzie, dan shekara 25, da Godspower Imafidion, dan shekara 25, a Satellite Town, Legas.

Ya bayyana cewa an kwace mota mai kirar Honda Accord 2007 wacce suka boye a unguwar Jemilugba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel