Gyara: Buhari ya bukaci hukumar PSC ta daidaita sahun rundunar 'yan sandan Najeriya

Gyara: Buhari ya bukaci hukumar PSC ta daidaita sahun rundunar 'yan sandan Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci mambobin hukumar kula da rundunar 'yan sanda (PSC) da su daidaita sahun rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) domin su inganta aikinsu na tabbatar da tsaro a kasa.

Shugaban kasar ya yi wannan kira ne a fadarsa a Abuja yayin da ya karbi rahoton hukumar PSC na shekarar 2018.

Ya bukaci mambobin su rubanya kokarinsu domin ganin rundunar 'yan sanda ta sauke nauyin da ke wuyanta.

"Hukumar ku na da kalubalen sa ido da kula da alhakin da aka dora a kan rundunar 'yan sanda.

"Na san kusan dukkan mambobin wanna hukuma, kuma yawanci sun san sirrin aiki, a saboda haka ina tsammanin zasu daidaita sahun rundunar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da nadin hadimai guda biyu da zasu yi aiki tare da Lai Mohammed

"Na yi imanin cewa babban sifeton rundunar 'yan sanda na yin iyakar kokarinsa. Matukar ba mu daidaita sahun rundunar 'yan sanda ba, ba zamu samu sukunin warware kalubalen tsaro da kasa ke fama da shi ba," a cewar shugaba Buhari, kamar yadda yake a cikin sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar.

Buhari ya ce alhakin hukumar PSC ne ta yi karin girma, bayar da mukami da ladabatar da jami'an 'yan sandan Najeriya, in banda babban sifeton rundunar.

Shugaban kasar ya kara da cewa duk da yana sane da irin kokarin da hukumar PSC ke yi wajen kawo gyara a aiyukan 'yan sanda, hakan ba zai hana ya bukaci su rubanya kokarinsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel