Majalisar Kano ta roki wani muhimmin alfarma daga wurin Ganduje

Majalisar Kano ta roki wani muhimmin alfarma daga wurin Ganduje

Majalisar Jihar Kano a ranar Talata ta yi kira ga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya gyra gandan da ta hada kananan hukumomi biyar a jihar kafin ta rushe.

Daily Nigerina ta ruwaito cewa dan majalisa mai wakiltan Rano daga jam'iyyar APC, Nurudeen Alhassan-Ahmed ne ya gabatar da batun gaban majalisa karkashin jagorancin Kakakin majalisa Abdulazeez Garba-Gafasa.

A cewarsa, gadan da ke garin Dan Hassan ya hada kanannan hukumomin Kura, Bunkure, Kibiya, Rano, Sumaila da Tundun wada na bukatar gyara cikin gaggawa.

"Muna son gwamnatin jihar ta taimakawa mutanen yankin cikin gaggawa domin rushewar gadan zai shafi tattalin arzikin kananan hukumomin.

"Halin da gadar ke ciki abin damuwa ne kuma hakan ya faru ne sakamakon ruwan sama mai yawa, mutanen garurruwan suna fuskantar irin hakan musamman a lokacin damina.

DUBA WANNAN: Nan da shekara 15 man fetur zai zama 'kayan kawai' - Gwamna Badaru

"Saboda haka ina kira ga Gwamna Abdullahi Ganduje ta taimaka wa mutanen garruruwan kafin ginin ya ruguje domin kada hakan ya shafi ayyukansu na noma da wasu ayyukan," inji shi.

Bayan tafka muhawarra kan batun da 'yan majalisar su kayi, majalisar ta amince da kira ga gwamnan jihar ya dauki mataki kan lamarin.

Kazalika, majalisar ta yi kira ga gwamnan ya gina gada a kauyen Romo dake karamar hukumar Bagwai na jihar.

Dan majalisa mai wakiltan Bagwai/Shanono daga jam'iyyar APC, Ali Ibrahim-Isa ne ya gabatar da batun gaban majalisa. Ya ce idan aka gina gadar da zai hade Dokadawa, Romo da Kiyawa duka a karamar hukumar Shanono, hakan zai taimaka wurin bunkasa tattalin arzikin garuruwan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel