Uwargidan Ganduje ta samu mukamin Farfesa daga wata jami’a

Uwargidan Ganduje ta samu mukamin Farfesa daga wata jami’a

Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha dake Nijar ta bayyana Dakta Hafsat Ganduje, uwargidan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Farfesa.

Uwargidan gwamnan dai tana koyarwa ne yanzu haka tsangayar ilimi ta Jami’ar Bayero dake Kano. Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ne ya fitar da wannan labari daga wani zancen da ya samu sanya hannun wanda ya assasa jami’ar Farfesa Abubakar Gwarzo.

KU KARANTA:Ministan sadarwa ya yi kira ga hukumar NITDA na ta kara zage dantse cikin ayyukanta

A cewarsa, wata tawaga mai girma daga jami’ar Maryam Abacha a karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Magaji-Rano ta kai wa Dr Hafsat wasikarta a gidan gwamnatin jihar Kano ranar 15 ga watan Satumba.

Sauran mambobin tawagar sun hada da; Farfesa Ibrahim Maigari da Dr Bala Muhammad Tukur. Da yake magana jim kadan bayan damkawa uwargidan gwamnan wasikar, Muhammad Tukur ya ce an karrama matar gwamnan da wannan matsayine saboda gudunmuwar da take bai wa cigaban ilimi.

“Ina mai farin cikin sanar da ke cewa hukumar gudunarwar Jami’ar Maryam Abacha ta aminta da daga matsayin zuwa matakin Farfesa tun daga ranar 14 ga watan Agusta, 2019.

“Samun wannan matsayin naki nada nasaba ne da irin gudunmuwar da kika jima kina badawa a bangaren cigaban ilimi.” Inji shi.

Ya kara da cewa, sabuwar dokar da Gwamna Ganduje ya kawo ta sanya ilimi kyauta kuma wajibi tun daga matakin firamare har zuwa sakandare, za ta taimaka kwarai da gaske wurin cigaban ilimi a jihar Kano.

Bugu da kari, “Shugaban hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya umarceni in sanar dake cewa, ya sanyawa data daga cikin dakunan kwanan dalibai mata na kwalejin koyar da ilimin kiwon lafiya da ke Kaduna sunan Farfesa Hafsat Ganduje.

“Duk wannan ba don komi ba sai domin karramawa gare ki da kuma tabbatar maki da cewa Jami’ar ba za ta taba mantawa da irin abinda kika yi mata ba.” Inji Tukur.

https://punchng.com/varsity-names-gandujes-wife-as-associate-professor/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel