Yanzu Yanzu: Buhari ya rushe kwamitin shugaban kasa kan kwato kadarorin gwamnati

Yanzu Yanzu: Buhari ya rushe kwamitin shugaban kasa kan kwato kadarorin gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rushe kwamitin shugaban kasa na musamman akan dawo da kadarorin gwamnati (SPIP) wanda Mista Okoi Obono-Obla ke shugabanta.

An umurci Atoni-Janar na tarayya kuka Ministan shari’a da yayi gaggawan karban duk wani bincike da ke kasa da sauran ayyukan SPIP din.

Muladdashin shugaban kasa na wancan lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kafa kwamitin a watan Agusta 2017, domin binciken lamuran da suka shafi rashawa, almubazaranci da sauran laifuffukan da jami’an gwamnati ke aikatawa.

Shugaban kasa Buhari ya mika godiya ga dukkanin mambobin kwanitin akan gudunmawarsu.

Shugaban kasar na duba zuwa ga karban rahoton karshe na hukumar ICPC akan binciken shugaban kwamitin da aka rushe wanda ke gudana.

A wani labarin kuma mun ji cewa Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kafa wata kwamiti da ta baiwa aikin kwato bashin naira tiriliyan 5 da wasu yan Najeriya 20 suka handame, inji rahoton jaridar Punch.

KU KARANTA KUMA: Mu na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankani lokaci kamar yadda China ta yi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da wannan kwamiti a ranar Talata, 17 gha watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel