Da duminsa: Amurka ta fasa kwai a kan harin da aka kai matatun man fetur a Saudiyya

Da duminsa: Amurka ta fasa kwai a kan harin da aka kai matatun man fetur a Saudiyya

Wani rahoto da kafar yada labarai ta BBC ta wallafa da yammacin ranar Talata ya bayyana cewa kasar Amurka ta gano wurin da aka yi amfani da shi wajen kai hari a kan matatun man fetur a kasar Saudiyya ranar Asabar.

An kai hare-haren ne ta hanyar aika wasu jirage masu sarrafa kansu da makamai masu linzami.

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Amurka ya shaida wa gidan talabijin din 'CBS News' cewa an harbo makaman da aka kai harin ne daga kuryar arewacin yankin Gulf da ke kasar Iran.

Kasar Saudiyya ta gaza dakatar da jiragen da suka kai harin ne saboda na'urorin kariyar da kasar ta daddasa domin kare kanta daga irin wadannan hare-hare na dakatar da harin da zai nufo kasar ne daga bangaren kudu, inda kasar Yemen take.

Dakarun sojin sama na Saudiyya sun fi mayar da hankali ne wajen kare kasar daga hare-haren kasar Yemen, abokiyar hamayyar ta kan iya kai mata.

Sai dai, tuni kasar Iran ta musanta zargin da ake yi mata na kai hari a kan matatun mai na kasar Saudiyya.

DUBA WANNAN: Korafin Aisha Buhari: EFCC ta fara binciken a kan tafka badakala a cikin shirin NSIP a jihohin arewa 2

A cikin wasu bayanan sirri da hotunan tauraron dan adam da kasar Amurka ta fitar, ta bayyana cewa akwai sa hannun kasar Iran a cikin harin da aka kai wa kamfanin Saudi Aramco.

Duk da 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen da ke samun goyon bayan kasar Iran sun dauki alhakin kai harin, kasar Iran ta musanta zargin cewa tana da hannu wajen kai harin.

A hirarsu da kafafen yada labarai na cikin gida da na kasa da kasa, wasu jami'an kasar Amurka da ba a bayyana sunansu ba sun ce basu yarda cewa 'yan tawayen Houthi ne suka kai harin ba bisa la'akari da girmansa.

Harin da aka kai wa matatun man na ksar Saudiyya ya janyo raguwar danyen mai a duniya da kaso biyar (5%) sannan kuma farashinsa ya yi tashin gwauron zabbi a kasuwar duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel