Majalisar Jihar Nasarawa ta musanta cewa ta kara yankuna da kauyuka a jihar

Majalisar Jihar Nasarawa ta musanta cewa ta kara yankuna da kauyuka a jihar

- Majalisar jihar Nasarawa ta musanta jita-jitar da ke yaduwa na cewa ta kara yankuna da kauyuka a jihar

- Kakakin majalisar ya bukaci gwamnatin jihar da ta nada kwamiti don bincikar zancen

- Abdullahi ya ce kirkira a binciko masu hannu a yada jita- jitar don su fuskanci fushin hukuma

Majalisar jihar Nasarawa ta musanta karin kauyuka da yankuna da ake yadawa cewa majalisar jihar tayi da kiran gwamnatin jihar da ta shirya kwamitin bincike akan hakan.

Kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi a ranar Talata ya ce, "Abin takaici ne ace wani zai zauna a ofishinsa, hankali kwance ya kirkiro da wannan takardar."

Ya shawarci jama'ar jihar da su yi watsi da jita-jitar da ke bayyanawa karuwar yankuna a jihar Nasarawa.

Abdullahi ya ce, "In har zababbun gwamnatin jihar nan na da bukatar kirkiro da wasu yankuna, ya dace su yi hakan ne da kyautattawa da adalci."

Ya bukaci jerin sunayen sabbin yankunan da kauyukan a mikosu Gaban majalisar jihar kamar yadda kundin tsarin mulki na 1999 ya baiwa majalisar jihar dam.

KU KARANTA: Tirkashi: Soja ya hallaka dan sanda har lahira

"Dole ne gwamnati ta shirya kwamitin bincike akan hakan don gano wadanda ke da sa hanni a aikata laifin tare da hukuntasu," inji shi.

Tuni dama dai 'yan majalisar jihar suka bayyana cewa basu da masaniya akan takardar da ke ta yawo a jihar. A hakan ne suka bukaci bincike tare da kawo masu laifin don fuskantar fushin hukuma.

An ruwaito cewa takardar shaidar kara yankuna da kauyuka a jihar Nasarawa an sa mata hannun ne tun a watan Mayu, 2019.

Lokacin da aka tunkari babban shugaban yada labarai na gwamnan jihar, Abdullahi Sule da zancen, bai maida martani akan hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel