Ministan sadarwa ya yi kira ga hukumar NITDA na ta kara zage dantse cikin ayyukanta

Ministan sadarwa ya yi kira ga hukumar NITDA na ta kara zage dantse cikin ayyukanta

Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami yayi kira ga hukumar NITDA da kuma sauran hukumomin dake karkashin ma’aikatarsa da su tashi tsaye domin cinma matakin ISO na kasa da kasa.

Ministan yayi wannan kiran ne yayin da ya ke gabatar da jawabinsa wurin taron bai wa hukumar NITDA shahadar ISO 27001; 2013 tsarin da ya samo asali tun lokacin da yake jagorantar hukumar ta NITDA.

KU KARANTA:Gwamnan Nasarawa ya rage yawan ma’aikatun gwamnati daga 18 zuwa 13

Bugu da kari, Ministan ya yabawa hukumar ta NITDA kasancewa hukuma irinta ta farko da ta samu wannan shahada ta ISO 27001; 2013. Inda ya ce: “Samun takardar shahadar abu guda ce a yayin da kuma kare martabarta shi ma aiki ne mai zaman kansa.”

A don haka, Dr Pantami yayi kira ga hukumar da ta cigaba da ayyukanta yadda ta saba ba tare da nuna gazawa ko gajiyawa ba, saboda akwai bitar ayyuka da za a rika yi lokaci zuwa lokaci, acewarsa.

Haka zalika, Ministan yayi karin haske a kan takardar shahadar inda ya bayyana ta da cewa takardar ce ta wadda take amfani a matakin kasa da kasa. “Ina marukar farin ciki ganin hukumar NITDA ta mallaki wannan takarda domin wannan zai ba ta damar dakile ayyukan ‘yan damfara ta hanyar yanar gizo.”

A bangare guda kuwa, Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi ya bai wa ministan tabbacin cewa hukumar ta sa a shirye take da yin aiki tare da ministan inda ya bayyana masa cewa, aiki za ayi ba tare da kasala ba kamar yadda dai aka saba.

https://www.nta.ng/news/technology/20190917-minister-of-communication-dr-pantami-tasks-nitda-to-meet-global-security-standard/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel