Hukumar NRC ta karyata rahoton harin yan bindiga a kan jirgin Abuja-Kaduna

Hukumar NRC ta karyata rahoton harin yan bindiga a kan jirgin Abuja-Kaduna

Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta musanta rahoton dake yawo a manhajar Whatsaspp da shafukan yanar gizo game da samuwar harin yan bindiga a kan jirgin Kaduna zuwa Abuja a makon data gabata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito hukumar ta karyata batun harin, inda ta bayyana shi a matsayin jita jita kawai, sa’annan ta yi kira ga matafiya da sauran jama’a dasu yi watsi da wannan rahoto, kamar yadda manajan jirgin Kaduna – Abuja ya bayyana.

KU KARANTA: Kungiyar Malaman Najeriya za su shiga yajin aiki na dindindin

Majiyar Legit.ng ta ruwaito manajan, Paschal A Nnorli yana cewa: “NRC na sanar da jama’a cewa babu wani hari da aka kai ma jiragen dake safara tsakanin Kaduna zuwa Abuja, muna sanar da fasinjojinmu cewa akwai tsauraran mataka tsaro da muka dauka don karesu.

“Muna mika godiyarmu ga jami’an tsaro, musamman rundunar Sojin Najeriya da rundunar Yansandan Najeriya saboda gudunmuwar da suke bamu wajen bada kariya ga jiragenmu da fasinjojinmu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta kawo wani sabon cikas ga kokarin kwashe yan Najeriya da rikicin kyamatar baki bakaken fata ya rutsa dasu a kasar Afirka ta kudu zuw Najeriya.

A wannan karo gwamnatin kasar ta haramta ma jirgin Najeriya, Air Peace daman sauka a filin sauka da tashin jirage domin kwashe rukuni na 2 na yan Najeriya da yawansu ya kai mutum 320.

Kamata ya yi jirgin Air Peace ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen Murtala Muhammad dake Legas tun a daren Litinin, amma har wayewar garin Talata, kamfanin bai samu sakon izinin sauka a kasar Afirka ta kudu daga hukumomin kasar ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel