Gwamnan Nasarawa ya rage yawan ma’aikatun gwamnati daga 18 zuwa 13

Gwamnan Nasarawa ya rage yawan ma’aikatun gwamnati daga 18 zuwa 13

Gwamnatin jihar Nasarawa ta rage yawan ma’aikatun gwamnati daga 18 zuwa 13 domin samun damar tafiyar da su yadda ya kamata.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ne ya bada wannan sanarwa wurin wani taron ganawa da masu ruwa da tsaki a Lafia babban birnin jihar jiya Litinin 16 ga Satumba.

Daga cikin ma’aikatun da aka soke tare da yi wasu maja da sabbin da gwamnatin ta kirkiro sun hada da; ma’aikatar ilimi na musamman, kimiyya da fasaha, ilimin gaba da sakandare, gidaje da kuma cigaban birane da ma’aikatar samar da ruwan sha.

Haka zalika sabbin ma’aikatun gwamnatin jihar guda 13 sun hada da; ma’aikatar Ilimi, Lafiya, Cigaban birane, Muhalli da albarkatun kasa, Matasa da wasanni, Shari’a, Kudi da kuma kasafin tattalin arziki.

Sauran sun hada da; ma’aikatar Kananan hukumomi, Hukumomi da cigaban ayyuka, Mata da walwalar al’umma, Gidaje da sufuri, Noma da ruwan sha, Kasuwanci, Sadarwa da kuma harkokin bude ido.

Gwamna Sule ya ce makasudin rage yawan ma’aikatun shi ne domin gwamnati ta samu damar kula da ko wace daya daga cikin ma’aikatun kamar yadda ya kamata.

Ya kuma kara da cewa, gwamnatinsa na kokarin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati a don haka yana bukutar goyon bayan masu ruwa da tsaki dake hukumomin domin cigaban jihar Nasarawa.

A wani labarin mai kama da wannan za kuji cewa, jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ta dakatar da Habubu Gwandu, daya daga cikin 'yan majalisar jihar ta Kebbi.

Kakakin jam'iyyar APC a jihar Kebbi, Alhaji Sani Dododo ne ya bada wannan sanarwar inda ya ce ana zargin dan majalisar ne da laifin zamba cikin aminci ga jam'iyyar APC kuma an kafa kwamitin bincike game da wannan al'amari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel