Yanzu-yanzu: Kasar Afirka ta Kudu ta bai wa jirgin Najeriya izinin sauka a kasarta – Ofishin jakadancin Najeriya

Yanzu-yanzu: Kasar Afirka ta Kudu ta bai wa jirgin Najeriya izinin sauka a kasarta – Ofishin jakadancin Najeriya

Labarin da muke samu a halin yanzu shi ne kasar Afirka ta Kudu ta bai wa jirgin Air Peace mai lamba B777 damar sauka a kasarta bayan da aka hana jirgin sauka a karon farko.

Jirgin dai ya taso ne daga kasar Najeriya zuwa Afirka ta Kudu domin kwaso mutane 320 ‘yan Najeriya zuwa kasarasu. Daya daga cikin jami’an ofishin jakadancin Najeriya a kasar Afirka ta kudun ne ya bada wannan labari a hirar tarho da kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN.

KU KARANTA:Kwamitin tattalin arziki: Wata jam’iyyar adawa ta yabawa Buhari a dalilin zaben Soludo

Mista Godwin Adama ya bada tabbacin cewa jirgin Najeriya mallakar kamfanin Air Peace ya samu izinin sauka kasar ta Afirka ta Kudu.

Mista Godwin Adama ya bada tabbacin cewa jirgin Najeriya mallakar kamfanin Air Peace ya samu izinin sauka kasar ta Afirka ta Kudu.

Godwin yayi magana wadda ta ci karo da maganar Allen Onyema wanda shi ke da kamfanin jiragen na Air peace. Inda ya ce rashin samun izinin sauka a kasar Afirka ta Kudu ya sanya jirginsu bai iya tasowa daga Legas ba da karfe dayan safe.

Amma sai dai kuma, Adama ya ce, jirgin ya samu izinin sauka amma babu damar dagawa Najeriya sai ranar Talata.

Adama ya cigaba da cewa: “Kasar so suke sai an tattaru wurin guda a cikin ranakun mako, a cikin tsakiyar dare za su bar nan.

“Ban dai san hakikanin lokacin da za su bar kasar (Afirka ta Kudu) nan ba, amma dai na san cewa tafiyar dare za su yi.

“Har yanzu ban sandalilin da ya sa suka hana jirgin sauka ba, amma dai na samu labarin cewa jirgin ya iso ne a cikin makararren lokaci.” Inji Godwin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel