Yanzu-yanzu: Direba ya kashe mutum biyu yayin da ya ke kokarin gujewa jami'an kwastam

Yanzu-yanzu: Direba ya kashe mutum biyu yayin da ya ke kokarin gujewa jami'an kwastam

Wani direba ya markade mutane biyu har lahira a kauyen Akinale da ke karamar hukumar Ewekoro na jihar Ogun a ranar Talata sakamakon mummunar gudu da ya ke yi domin ya dauko harmatattun kaya a motar kuma jami'an kwastam na biye da shi.

The Punch ta ruwaito cewa jami'an kwastam ne ke biye da direban da ya dauko tolotolo a hanyar Abeokuta zuwa Legas inda ya bi ta kan mutane biyu cikinsu har da makanike mai gyaran mota.

A hirar da ya yi da majiyar Legit.ng, Sarkin garin Akinale, Oba Olufemi Ogunleye ya ce direban da jami'an kwastam din duk suna da laifi a afkuwar lamarin.

Oba Ogunleye ya ce makaniken da aka kashe mutum ne da ke aikinsa tsakaninsa da Allah kuma sananne ne a garin.

KU KARANTA: Nan da shekara 15 man fetur zai zama 'kayan kawai' - Gwamna Badaru

Ya ce, "Hatarin da ya faru a yau abin takaici ne da bakin ciki.

"Akwai rashin da'a a bangaren direban kuma akwai rashin da'a a bangaren hukumar gwamnati domin ya kamata jami'an na kwastam su kama shi tun a kan iyakar shigowa kasa ba su rika bin direbobi cikin gari ba.

"Jami'an kwastam din ne suka biyo direban amma da hatsarin ya afku sai suka tsere. Babu wanda ya tsaya."

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

Oyeyemi ya ce, "Da gaske ne cewa jami'an kwastam suna bin wani mutum a cikin motar kirar bas kuma motar da kwace masa ya kashe mutane biyu."

Mai magana da yawun kwastam na jihar, Abdullahi Maiwadah ya ce zai yi bayyani da zarar ya samu cikaken bayani a kan abinda ya faru.

Ya ce, "A kan batun da ka ke tambaya, mun fara bincike. Zan neme ka da zarar na samu cikaken bayani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel