Korafin Aisha Buhari: EFCC ta fara binciken a kan tafka badakala a cikin shirin NSIP a jihohin arewa 2

Korafin Aisha Buhari: EFCC ta fara binciken a kan tafka badakala a cikin shirin NSIP a jihohin arewa 2

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya ce hukumarsa ta fara gudanar da bincike a kan zargin tafka almundahana da badakala a cikin shirin bayar da tallafi NSIP (National Social Intervention Programmes) a jihohin Borno da Yobe.

Magu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shi a cikin harshen Hausa da aka yi a gidan rediyon 'Peace FM' da ke garin Maiduguri.

Uwargida Mayram Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan bayar da tallafi, ita ce ke kula da shirin NSIP.

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta taba yin zargin cewa shirin ya gaza yin tasiri a yankin arewa.

Magu, wanda ya samu wakilcin Hamza Ridwan, mataimakin shugaban EFCC na shiyyar Maiduguri, ya ce sun fara bincike a kan shirin ne bayan samun korafe-korafe a kan yadda ake gudanar da harkokin da suka shafi shirin a lullube.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da nadin hadimai guda biyu da zasu yi aiki tare da Lai Mohammed

"Bayan mun samu korafe-korafe masu yawa a kan yadda ake gudanar da shirin a lullube, EFCC tare da hadin gwuiwar wasu masu ruwa da tsaki ta fara binciken kunbiya-kunbiyar da ake zargin ana yi a cikin shirin N-SIP, musamman harkar ciyar da daliban makarantun firamare.

"Hukumar EFCC na daga cikin masu ruwa da tsaki a cikin harkokin gudanar da shirin N-SIP, kuma yanzu ta fara binciken almundahanar karkatar da kudaden tallafa wa manoma da sauran bangarorin shirin a jihohin Borno da Yobe,'' a cewarsa.

Shugaban hukumar na EFCC ya bukaci jama'a da su basu muhimman bayanai da zasu taimaka musu a binciken da suka fara tare da bayyana cewa zasu gurfanar da duk wanda suka samu da hannunsa a ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel