Kwamitin tattalin arziki: Wata jam’iyyar adawa ta yabawa Buhari a dalilin zaben Soludo

Kwamitin tattalin arziki: Wata jam’iyyar adawa ta yabawa Buhari a dalilin zaben Soludo

Shugaban jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA na kasa, Dr Victor Ike Oye ya taya tsohon shugaban babban bankin Najeriya (CBN), murnar zabensa a matsayin daya daga cikin mambobin kwamitin bai wa shugaban kasa shawara game da tattalin arziki.

Oye ya fadi wannan maganar ne a Abuja ranar Talata 17 ga watan Satumba inda ya bayyana zaben Soludo a matsayin zabe mai kyau a daidai lokacin da ake bukatarsa.

KU KARANTA:Sarki Sanusi ya yabawa Buhari game da nadin sabon kwamitin tattalin arziki

Oye ya kara da cewa: “Ga masu gutsuri tsoma da ce-ce kuce game da nadin Soludo kasancewarsa jigo ne a jam’iyyar APGA, sai su shiga hankalinsu. Ba maganar jam’iyya ce ta sa muke yabawan zaben nasa ba.”

Bugu da kari, Soludo zai yi aiki tukuru kasancewar a baya yana daya daga cikin wadanda suka taimakawa tattalin arzikin kasar nan a lokacin da yake neman durkushewa, a cewarsa.

A karshe kuma ya jinjinawa Shugaba Buhari a kan wannan zaben da yayi inda ya bayyana zaben a matsayin zabe mai kyau wanda ake da matukar bukatarsa.

A wani labari mai kamar wannan zaku ji cewa, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido II ya yabawa Shugaba Buhari game da nadin kwamitin shawari game da tattalin arzikin Najeriya.

Sarki Sanusi ya bayyana zaben wadannan mutanen a matsayin abu mafi amfani daga cikin ayyuka Shugaban kasa tun da aka rantsar da shi a wa’adi na biyu.

Dukkanin mutanen da Shugaban kasa ya zaba kwararru kuma akwai yakinin cewa za su yiwa tattalin arziki abinda yake bukata domin kaucewa durkushewa, a cewar Sarki Lamido.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel