Wata sabuwa: Kasar Iran tace ba za ta tattauna da Amurka ba

Wata sabuwa: Kasar Iran tace ba za ta tattauna da Amurka ba

Babban jigon kasar Iran, Ayatollah Khamenei a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, ya bayyana cewa jami’an kasar sun yanke hukuncin kin tattaunawa da Amurka a kowani mataki.

An tattaro Khamenei na fadi a shafinsa na yanar gizo cewa “ta hanyar tattaunawa, yan Amurka na neman tursasa bukatunsu akan Iran da kuma tabbatar da tasirin cikakken kamfen dinsu.”

Yace kamfen din Washington akan yan kasar Iran ya gaza cimma manufarsa.

A cewarsa, tattaunawa da Amurka zai yiwu be kawai cikin tsarin kungiyar P5+1 wanda ya hada da mambobin dindindin guda biyar na kwanitin tsaro na majalisar dinkin duniya da kuma Jamus.

Khamenei yace Washington ta dawo da yarjejeniyar nukiliyar Iran na 2015 da ta yasar a 2018, idan har Amurka na son kowani irin tattaunawa.

Kakakin Ma’aikatar kasar waje na Iran ma yayi magana a ranar Litinin inda shima yace babu wata tattaunawa tsakanin Iran da shugabannin kasar Amurka a taron majalisar dinkin duniya mai zuwa a New York.

KU KARANTA KUMA: NECO ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 a Neja saboda bashi

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya janye kasar daga yarjejeniyar Nukiliyar Iran na 2015 a watan Mayun 2018 kan hujjar cewa yarjejeniyar ba cikakke bane.Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel