Buhari ya amince da nadin hadimai guda biyu da zasu yi aiki tare da Lai Mohammed

Buhari ya amince da nadin hadimai guda biyu da zasu yi aiki tare da Lai Mohammed

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sake nada Segun Adeyemi da Williams Adeleye da zasu aiki a ofishin Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, a matsayin mataimaka na musamman a bangaren yada labarai.

A cikin wasikar basu mukamin, mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, an bayyana cewa an dauki hadiman aiki ne ranar 6 g watan Satumba, 2019, kamar yadda sanarwa daga ma'aikatar yada labarai da al'adu ta bayyana.

Adeyemi da Williams sun taba rike irin wannan matsayi daga watan Nuwamba na shekarar 2015 zuwa watan Mayu na shekarar 2019.

A wani labarin na Legit.ng, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankanin lokaci kamar yadda kasar China ta yi.

Da take magana ranar Litinin a wurin wani taro a Abuja, Zainab ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen kaddamar da wasu aiyuka da zasu saka Najeriya cikin jerin kasashen duniya 100 da yin kasuwanci ke da sauki.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe Muhammad Bayero, basarake a karamar hukumar Mangu

Najeriya na mataki na 146 a cikin jerin kasashen duniya da yin kasuwaci ke da sauki a shekarar 2018 bayan ta fado daga mataki na 145 da take kai a shekarar 2017.

Ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta dauki matakan da zasu saka Najeriya ta zama abar kauna ga masu son saka hannun jari.

Ta ce daga cikin irin wadannan matakai akwai kafa hukumar saukaka yin kasuwanci PEBEC (Presidential Enabling Business Environment Council) domin bayar da tallafi ga duk wani yunkurin fadada harkokin kasuwanci.

Zainba ta ce matsayin Najeriya a jerin kasashen zai kara matsa wa sama da zarar gwamnati ta kaddamar da wadannan manufofi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel