Da dumi dumi: Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta hana jirgin Najeriya daukan yan Najeriya

Da dumi dumi: Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta hana jirgin Najeriya daukan yan Najeriya

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta kawo wani sabon cikas ga kokarin kwashe yan Najeriya da rikicin kyamatar baki bakaken fata ya rutsa dasu a kasar Afirka ta kudu zuw Najeriya, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a wannan karo gwamnatin kasar ta haramta ma jirgin Najeriya, Air Peace daman sauka a filin sauka da tashin jirage domin kwashe rukuni na 2 na yan Najeriya da yawansu ya kai mutum 320.

KU KARANTA: Gwamna Umahi zai nada mutane 800 a matsayin masu bashi shawara

Kamata ya yi jirgin Air Peace ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen Murtala Muhammad dake Legas tun a daren Litinin, amma har wayewar garin Talata, kamfanin bai samu sakon izinin sauka a kasar Afirka ta kudu daga hukumomin kasar ba.

Idan za’a tuna a ranar Larabar data gabata ne kamfanin Air Peace ta kwashe yan Najeriya 178 daga kasar Afirka ta kudu, wanda ta dawo dasu gida Najeriya, amma ko a wannan lokaci sai da jami’an hukumar shige da fice na kasar suka yi kokarin kawo ma aikin matsala.

Shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeam ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda yace duk kokarin da kamfanin ta yi na samun izinin sauka a kasar Afirka ta kudu hakan bai yiwu ba.

“Bamu tashi da karfe 1 na dare kamar yadda muka shirya ba saboda rashin wannan izini, ma’aikatanmu sun jira har karfe 3 na dare suna jiran wannan izini, amma da muka ga abin ba yanzu zai zo ba, sai suka koma dakunansu a Otal, amma dai muna sa ran komai zai wuce.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel