Dogaro da kai: Gwamnatin kasar Amurka za ta tallafa wa mata miliyan 15 a Najeriya

Dogaro da kai: Gwamnatin kasar Amurka za ta tallafa wa mata miliyan 15 a Najeriya

Gwamnatin kasar Amurka za ta bayar da tallafi ga mata miliyan 15 da ke da sana'o'i a Najeriya da sauran sassan duniya daga yanzu zuwa shekarar 2025.

Da take magana ranar Litinin a wurin wani taro da aka shirya domin mata 'yan kasuwa a jihar Legas (AWE), Claire Pierangelo, wakiliyar gwamnatin kasar Amurka, ta ce bawa mata damar bunkasa harkokinsu na kasuwanci zai taimaka musu wajen fita daga kangin talauci sannan kuma zai inganta tattalin arzikin kasa.

Ta ce an bullo da shirin AWE ne domin bawa kasashe masu taso wa damar bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar tallafa wa mata 'yan kasuwa wajen basu horo da koyar da su dabarun kasuwanci na zamani.

Ta kara da cewa an tsara shirin AWE ne domin inganta rayuwar mata ta fuskar tattalin arziki, tsaro da cigabansu a cikin rayuwa.

DUBA WANNAN: Mu na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankani lokaci kamar yadda China ta yi

Ta bayyana cewa shirin AWE zai bayar da tallafi ga mata a kasashe 26 da suka hada da Najeriya, a mataki na farko na shirin.

A cewar ta, shirin zai bayar da tallafi da horo a kan yadda mata a kalla 100, masu shekaru 18 zuwa 45, a jihar Legas zasu yi kasuwanci cikin sauki da nasara.

Shirin zai fara da mata 100 kuma za a gayyato masana da suka yi shura a harkokin kasuwanci domin basu ilimi da koya musu dabarun samun nasara a kasuwanci.

Shugabar kaddamar da shirin a Najeriya, Uwargida Inya Lawal, ta ce an zabo mata 100 ne daga cikin mata fiye da 600 da suka nuna sha'awar cin moriyar shirin domin fara yin gwaji da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel