Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra

Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra

- Sama da mutane 300 ne a kauyuka 6 na karamar hukumar Awambia suka rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa

- Ambaliyar ruwan hadi da zai-zayar kasa sun kwashe harda titin gidan Dan majalisar yankin

- Mutanen yankin sun hada sama da miliyan 800 don kawo karshen matsalar muhallin ba tare da ko sisin gwamnati ba

Fiye da iyalai 300 ne a kauyuka 6 suka rasa gidajensu a karamar hukumar Amawbia dake jihar Anambra sakamakon ambaliyar ruwa.

Ambaliyar tare da zai-zayar kasa ta shafi kauyuka da dama inda ta datse hanyoyin da ke tsakaninsu da biranen da suke da makwaftaka dasu irin su Nise, Nibo, Umuokpu da Agukwu Nnri.

Zai-zayar kasar ta hana yara zuwa makarantunsu.

Hakazalika, yara biyu ne suka tsallake rijiya da baya sanadin ambaliyar domin kiris da ruwan yayi gaba da su.

Ambaliyar ruwa da zai-zayar kasa ta kwace a cikin jihar Anambra inji daraktan CEMA Okey Maduforo, na jihar.

KU KARANTA: Tirkashi: Soja ya hallaka dan sanda har lahira

"Akwai bukatar gwamnati ta tallafawa mutanen yankin da gaggawa."

Maduforo ya kara da cewa "Matanen Awambia da mazauna wajen sun kashe sama da naira miliyan 800 a shekaru 7 da suka gabata don yakar matsalolin muhalli ba tare da tallafin gwamnati ba."

Sauran yankunan da zai-zayar kasar ta shafa ya hada da: Makarantar sakandare ta Union, Kwalejin Kabe, Otal din May Rose, inda duk hanyoyin da zasu kai garesu sun lalace.

Zai-zayar kasar da ambaliyar ruwan sun datse hanyar zuwa gidan Dan majalisar jihar mai wakiltar Awka ta kudu, Chukwuma Okoye.

Har lokacin rubuta wannan rahoton ba a samu magana da dan majalisar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel