Wadume: Jami’an tsaron Najeriya sun rasa inda za su gaba bayan damke mai laifi

Wadume: Jami’an tsaron Najeriya sun rasa inda za su gaba bayan damke mai laifi

Sojojin Najeriya da kuma ‘Yan sandan kasar ba su iya cin ma maslaha ba game da maka fitaccen wanda ake zargi da laifin nan watau Hamisu Bala wanda jama’a su ka fi sani da Wadume.

Kamar yadda labari ke zuwa mana daga jaridar The Nation a yau, Sojoji da ‘yan sanda sun shiga rudani wajen binciken Wadume bayan da aka nuna cewa akwai hannun Soji a ta’adin da Wadume ya ke yi.

‘Yan Sanda sun kama Hamisu Bala kwanakin baya ne, amma wasu Sojoji su ka far masu inda su ka saki wanda ake zargi da laifin. Daga baya dai jami’an ‘yan sandan sun sake damke Wadume a Garin Kano.

Rundunar Sojin Najeriya ta binciki lamarin, amma ana ta boye rahoton binciken da sunan cewa na sirri ne. Haka kuma Sojojin kasar sun ki sakin jami’an su da ake zargi da laifi domin a hukuntasu.

Bisa dukkan alamu, Sojojin Najeriya ba su da niyyar sakin jami’an na su da aka samu da laifi a hannun ‘yan sanda wanda alhakin gurfanar da marasa gaskiya a gaban kotu ya rataya kan wuyansu.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun fito da wasu Kananan yara da su ka dauke

Bayan Wadume, akwai akalla mutum 13 da ake zargi da laifin da ke da alaka da shi. Kawo yanzu dai jami’an tsaro sun rasa yadda za su shawo kan wannan matsala domin a fara bincike a gaban kuliya.

Wata majiya tace idan aka cigaba da tafiya a haka, za a dade ba kai ga zuwa kotu ba. Dama can akwai wata ‘yar tsama tsakanin ‘yan sanda da sojoji inda ake yawan samun rashin jituwa tsakaninsu.

Kakakin ‘yan sanda, Frank Mba, ya ki amsa tambayar da aka yi masa game da abin da ya hana a gurfanar da Wadume a kotu har yanzu. Mba yace kwamitin da su ka binciki lamarin ne su ke da masaniya.

Mba ya tabbatarwa Manema labarai cewa Wadume ya na hannun jami’an tsaro. Amma bai bayyana hannun wadanda ya ke ba a tsakanin sojoji ko ‘yan sanda, sannan ya ki bayyana inda yake tsare.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel