Majalisar wakilai ta gano 'yan kwangila 1,723 da suka karba N70b suka yi muqus

Majalisar wakilai ta gano 'yan kwangila 1,723 da suka karba N70b suka yi muqus

- Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai akan aiyukan da ba a kammala ba a yankin Niger Delta ya gano 'yan kwangila 1,723 da suka amshe naira biliyan 70.495 ba tare da sunyi aikin komai ba

- Daraktan binciken kudaden da aka kashe na tarayya ya sanar da kwamitin cewa 90% na kwagilolin an badasu ne a tsakanin 2011 zuwa 2012.

- Rahoton ya sanar cewa wannan abun ya zama ruwan dare na karbar kudi ba tare da aiki ba

- Kamar yadda auditan ya sanar, matukar aka cigaba da tafiya da irin wadannan mutanen a hukumar NDDC toh kuwa yanzu ma aka fara

Kudi har naira biliyan 70.495 ne aka mika ga 'yan kwangila 1,723 da suka ki yin aiki inji kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai akan aiyukan da ba a kammala ba na yankin Niger Delta.

An gano hakan ne bayan da daraktan binciken kashe kudi na tarayya ya sanar da kwamitin a zaman da suka yi a satin da ya gabatar.

Legit.ng ta gano cewa, a rahoton da daraktan bincken kashe kudi na tarayya ya mikawawa kwamitin, ya nuna N70,495,761 ne 'yan kwangila 1,723 suka lashe ba tare da aikin komai ba.

Rahoton yace: "kashi 90 cikin 100 na wadannan kwangilolin a bada su ne a tsakanin 2011 da 2012. Yakamata a bayyanawa kwamitin cewa, wasu daga cikin 'yan kwangilar sun kalmashe kudaden fara aiki na kwangiloli 3 zuwa 4 ba tare da an gansu a inda yakamata suyi aikin ba."

"Hakan kuwa ya zama dalilin da yankin har yau ya kasa samun cigaba. Laifin ba wai 'yan kwangilar kadai za a baiwa ba, har da hukumar NDDC, da suka mika kwangila ba tare da anyi ta ba."

"An gano cewa 50% na 'yan kwangilar da suka yi ikirarin sun aiwatar da aikin da suka karba kudinsa, an gano cewa karbe kudin kawai suka yi tare da lamushewa ba tare da yin aikin ba."

KU KARANTA: Tirkashi: Soja ya hallaka dan sanda har lahira

Daraktan binciken kudaden yace matukar za a cigaba da baiwa hukumar NDDC irin shuwagabannin da suke da su a da, toh tabbas hakan zata cigaba da aukuwa.

Legit.ng ta gano cewa mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya baiwa 'yan kwangilar kwana 30 da koma kan aiyukansu ko kuma su fuskanci shari'a.

Mataimakin shugaban kasar ya ce matukar 'yan kwangilar basu koma kan aiyukansu ba, toh tabbas zasu gamu da hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Ya kara da bada umarnin mika jerin sunayen 'yan kwangilar da suka karbe kudin ba tare da aiki ba ga ma'aikatar shari'a da kuma hukumar yaki da rashawa ta EFCC don bincike da hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel