Za mu hukunta wadanda suka fallasa wasika kan bayanan asusun manyan jami’an gwamnati - NFIU

Za mu hukunta wadanda suka fallasa wasika kan bayanan asusun manyan jami’an gwamnati - NFIU

Hukumar da ke kula da kudade ta Najeriya wato NFIU tace tana bincike akan yadda fallasa wasikarta zuwa ga bankunan zamani, inda suka bukaci bayanan asusun manya jami’an gwamnati.

A wai jawabi a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, Ahmed Dikko, Shugaban NFIU, ya bayyana rahoton cewa hukumar na binciken Shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai da Shugaban alkalan Najeriya a matsayin kanzon kurege.

Dikko yace wasikar hukumar da aka fallasa zuwa ga bankuna inda ta bukaci bayanan asusun manyan jami’an gwamnati abune da ta saba gudanarwa domin kare kudaden gwamnati da kadarorinta.

Yace hukumar na bincike kan yadda wasikar ta bazu sannan kuma cewa za a hukunta wadanda suka aikata laifin fallasa wasikar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Farasin kayayyaki ya sauka duk da rufe iyakar kasar – Hukumar kididdiga ta kasa

A baya mun ji cewa Hukumar kula da kudade ta NFIU ta soma gudanar da bincike a kan asusun bankin shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad da mataimakinsa Ovie Omo-Agege.

NFIU ta fara gudanar da wani bincike game da asusun bankin da shugabannin majalisar dokokin ke ajiyar kudi.

Wadanda wannan binciken ya shafa sun hada da; Shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, mataimakin kakakin majalisar wakilai Idris Wase da sauran masu rike da mukamai a cikin majalisun biyu.

Hukumar tana kan gudanar da irin wannan binciken game da asusun bankin Alkalin-alkalan Najeriya, Jastis Muhammad Tanko.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel