Illolin gishiri mara sinadarin 'Iodine'- NAFDAC

Illolin gishiri mara sinadarin 'Iodine'- NAFDAC

- Hukumar NAFDAC ta bayyana dalilan da zasu sa a guji gishiri mara sinadarin 'Iodine'

- Daraktan hukumar ya bayyana jihar Nasarawa a matsayin jiha mai yankuna har hudu da ake samar da gishirin mai illa

- Daga cikin illolin gishirin ya hada da kawo cutar makoko

Hukumar NAFDAC ta shawarci 'yan Najeriya da su gujewa shan gishiri mara sinadarin 'Iodine' cewa "Akwai hatsari ga lafiyar Dan Adam."

Dr Abubakar Jimoh, daraktan hulda da jama'a na hukumar ya bada shawarar nan yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai a Abuja ranar Talata.

Daraktan ya bada shawarar ne yayin maida martani game da jita-jitar cewa har fa yanzu mutanen karkara na cigaba da shan gishirin da ba a tace ba.

Ya ce, shan irin wannan gishirin na iya kawo makoko da sauran cutuka masu hadarin gaske ga rayuwar Dan Adam. A don haka ne ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji irin kayayyakin nan.

KU KARANTA: Ko kunsan dalilin kama mawaki Naziru M. Ahmad?

Kamar yadda daraktan ya sanar, akwai yankuna hudu a Najeriya da ake yin gishirin gargajiyar, yankuna ne a jihar Nasarawa.

"Hukumar NAFDAC na kokarin hana siyar da irin wannan gishirin amma sun ki dainawa."

"Bayan kirkirar hukumar NAFDAC a 1993, har yanzu akwai sauran jiga-jigan aiyukan da za a yi akan irin wannan gishirin. Mun shirya taron wayar da kai. Ana ilimantar da mutane akan illolin gishirin gargajiya mara sinadarin 'Iodine'."

Hukumar ta fara shirin wayar da kai na hadin guiwa da UNICEF akan sinadaran da jiki ke bukatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel