Bayan kin karbar mukamin da PDP ta ba Melaye, ya yi magana kan makomar Yahaya Bello a zabe mai zuwa

Bayan kin karbar mukamin da PDP ta ba Melaye, ya yi magana kan makomar Yahaya Bello a zabe mai zuwa

- Sanata Dino Melaye yace babu shakka Yahaya Bello ba zai koma kujerarsa ba

- Melaye ya kara da cewa ko sau nawa za a yi zabe, zai kara maka Smart Adeyemi da kasa

- Ya musanta cewar da aka yi zai hadu da Gwamna Yahaya Bello

Sanata Dino Melaye ya ce babu shakka Gwamna Yahaya Bello zai fadi a zaben kujerar gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa dan majalisar Kogin ya musanta labarin cewa zai bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC bayan da ya fadi zaben fidda gwanin da aka yi a jiharsa.

Melaye ya kara da cewa babu zaben sanata da za a kara yi don yana da tabbacin zai maka Adeyemi da kasa in har aka kara.

Akwai jita-jita da ke ta yawo cewa dan majalisar na shirin komawa jam'iyyar APC don rike kujerarsa ta sanata.

KU KARANTA: Ko kunsan dalilin kama mawaki Naziru M. Ahmad?

Rahoton ya kara da bayyana cewa Melaye zai hadu da gwamna Yahaya Bello amma dan majalisar ya musanta hakan.

Ya ce: "Duk karya ne. Bazan iya haduwa da Yahaya Bello ba. Kuma dole ne ya sauka. Zan kada Smart a koyaushe duk da ma ba wani sabon zabe da za a kara yi."

"Adeyemi rudadden mutum ne wanda kosawa ta shafe tunaninsa. Marigayi ne a siyasa."

Idan zamu tuna, Melaye ya ki karbar matsayin shugaban yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP.

Mun samu rahoton cewa sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya sanar cewa an zabi Melaye a matsayin shugaban yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar Kogi karkashin jam'iyyar PDP. Dan majalisar ya yi wa jam'iyyar fatan alheri amma yaki karbar mukamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel