NIHSA ta sake lissafa wasu jihohi 13 da matsananciyar ambaliyar ruwa zai shafa

NIHSA ta sake lissafa wasu jihohi 13 da matsananciyar ambaliyar ruwa zai shafa

Direktan Hukumar kula da lamuran ruwan sama da na koguna (NIHSA), Clement Eze, a ranar Litinin ya ce wasu karin johohi 13 za su fuskanci ambaliyar ruwa saboda kara cika da rafin Benue da na Neja su kayi kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

A jawabin da ya yi yayin wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, ya ce jihohin Kebbi, Niger, Kwara, Nasarawa, Kogi, Edo, Anambra, Delta, Rivers, Bayelsa, Adamawa,Taraba da Benue za su kasance cikin jihohin da ambaliyar zai shafa saboda kara cika da rafin Benue da ke saboda ruwan sama da kuma ruwa da ke kwararowa daga wasu rafin.

Ya ce ruwa daga shida cikin kasashe tara na 'Niger Basin Authority' yana kwararowa cikin Najeriya kuma hakan na iya janyo matsananciyar ambaliya a jihohin da aka lissafa.

Ya ce Najeriya na cikin shirin ko ta kwana saboda ana tsamanin ambaliyar ruwar da aka gano a Jamhuriyar Nijar zai iso Najeriya ta cikin jihar Kebbi a jiya.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wani babban jami'in dan sanda ya rasu a Sokoto

A baya Hukumar ta mika gargadi ga wasu jihohi 15 da suka hada da Niger, Lagos, Edo, Imo, Abia, Jigawa, Adamawa, Delta, Rivers, Cross Rivers, Oyo, Enugu, Kebbi, Nasarawa, Bauchi da kuma babbar birnin tarayya Abuja.

Eze ya yi kira ga cewar akwai bukatar yin tsarin haka manyan magudanar ruwa, da kuma guje ma gina gidaje a wuwaren da ruwa ke gudana da kuma gina wuraren kula da ambaliar ruwa a kasar da makwabta.

Ya ce amaliyar ruwa na iya zama annoba idan babu abubuwan da ake bukata domin magance shi a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel