Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a hanyar babban titin Delta

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a hanyar babban titin Delta

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wasu adadin mutane da ba a sani ba a yankin Uvwiamuge da ke Ughelli/Agbarho na hanyar gabas maso yamma, a karamar hukumar Ughelli a jihar Delta.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin wanda ya shafe tsawon minti 30, ya afku ne da misalin karfe 6:40 na yammacin ranar Litinin, 16 ga watan Satumba.

A wannan wurin ne aka sace wasu mutane, ciki harda hadimin wani babban malamin coci, Simeon Okah watanni biyu da suka gabata. Sannan aka sake su bayan an biya kudin fansa.

Idon shaida sun bayyana cewa yan bindigan wadanda yawansu ya kai kimanin su 20, sun tsere daga wajen bayan sun yi musayar wuta da yan sanda.

A cewarsu, yan bindigan sun yi garkuwa da akalla mutane takwas.

Amma wasu daga cikin masu wucewa sun yi ikirarin cewa mutane hudu kawai yan bindigan suka sace sannan suka yi hanyar daji da su.

Masu mota sun yasar da motoci da dama yayinda sauran suka juya da gudun domin guje ma fadawa hannun yan ta’addan.

An tattaro cewa akalla jami’an yan sanda 30 suka isa wajen bayan afkuwar lamarin.

KU KARANTA KUMA: Aisha Umar Ardo ta dawo gida bayan an biya masu garkuwa kudin fansa

Kwamishinan yan sanda, Mista Adeyinka Adeleke, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa tuni aka fara gudanar da bincike.

Sai da kuma ya bayyana cewa mutum daya kawai aka sace, yayinda jami’ansa suka fito kan lokacin domin daidaita lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel