Majalisar zartarwar ECOWAS ta roki Najeriya da ta bude iyakokinta

Majalisar zartarwar ECOWAS ta roki Najeriya da ta bude iyakokinta

- Majalisar zartarwa ta kungiyar tattalin arzikin Afirka ta roki Najeriya akan rufe iyakokinta da tayi

- Kakakin majalisar ya bukaci sauran kasashen da su mutunta dokokin yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen

- Majalisar ta kushe kisan 'yan wasu kasashe da ake a kasar Afirka ta kudu, ganin cewa hakan na iya kawo rarrabuwar kai a Nahiyar Afirka

Majalisar zartarwa ta kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ta roki gwamnatin Najeriya da ta bude iyakokinta da ta rufe.

Kakakin majalisar, Hon. Moustapha Cisse Lo, ya yi wannan kiran ne a taron majalisar zartarwar kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma kashi na biyu da aka yi a Monrovia, Liberia.

Ya kara da cewa, rufe iyakokin ya zama barazana ga yarjejeniyar shiga da ficen da ke tsakanin kasashen. Kuma hakan yazo ne a lokacin da Afirka ke bukatar kokarin cire duk wani shinge tsakanin kasashenta.

Cisse Lo, ya jawo hankalin gwamnatin Najeriya da ta kawo hanyar shawo kan shigo da kaya ba bisa ka'ida ba a maimakon kulle iyakokin. Yace hakan ba hanya ce mai bullewa ba.

KU KARANTA: Ko kunsan dalilin kama mawaki Naziru M. Ahmad?

"Rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Benin wanda yafi wata daya da kuma rufe iyakar kasar Nijar babban kalubale ne game da amfanin kungiyar wajen kawo wanzuwar zaman lafiya da amana."

"Majalisar zartarwa ta ECOWAS na kira ga kasashen da su dage wajen bin dokar makwaftansu wajen fada da shigo da kayayyaki ba bisa ka'ida ba."

"Dole ne a duba tushen matsalar nan don kawo karshenta na dindindin," inji shi.

Kakakin majalisar ya kara da kushe harin da 'yan kasar Afirka ta kudu ta ke kaiwa 'yan Najeriya, ganin cewa hakan babbar barazana ce ga hadin kan Nahiyar Afirka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel