Ka kai can, ba ma so - Gwamnatin jihar Kwara ta mayarwa Saraki kyautan da yayi wa yan makaranta

Ka kai can, ba ma so - Gwamnatin jihar Kwara ta mayarwa Saraki kyautan da yayi wa yan makaranta

Makarantun jihar Kwara ba zasu karbi wani kyautan kayan karatu da hotunan mutum a jiki ba, sakataren din-din-din na ma'aikatar Ilimin jihar Kwara, Yakub K. Aliagan, ya laburta.

Wannan ya biyo bayan rahoton cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya baiwa makarantun jihar kyautan kayayyakin karatu dauke da hotunansa a jiki.

Rahotannin kafofin sadarwa sun nuna cewa makarantun sun mayarwa dan siyasan kyaututtukansa kuma an yi kira da gwamnatin jihar tayi tsokaci a kai.

Amma da gwamnatin ta tofa albarkacin bakinta, ta bayyana cewa ba'a biyo da kayayyakin ta hannunta ba.

Jawabin yace: "Abinda ya kamata yayi shine ya aika da kayayyakin ma'aikatar ilimi da ke da hakkin tantance abubuwa kafin rabawa makarantu."

"Rashin yin wannan kadai ya sabawa doka, kuma bin doka na da muhimmanci wajen karfafa ma'aikatunmu."

"Bugu da kari, bai halalta ga kowani ma'aluki ba ya manna hotunansa ko tambari kan kayayyakin da aka saya da kudin gwamnati, domin rabawa makarantu ba."

Ya bayyana hakan ne saboda gwamnatin tarayya ce ta bada kudin sayan kayayyakin ga gwamnatin da ta shude.

Ya kara da cewa: "Ya kamata a sani cewa ma'aikatar ilimin jihar ya tuntubi gwamna Abdulrahman Abdulrazak kan wallafa takardun makaranta dauke da hotonsa amma ya kiya."

"Yace bai kamata gwamna ya sinya hotunansa kan kayayyakin da aka saya da kudin al'umma ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel