Tashin hankali: An yiwa wani dan karamin Wada dukan kawo wuka, bayan ya sace wa wani mutumi mazakuta

Tashin hankali: An yiwa wani dan karamin Wada dukan kawo wuka, bayan ya sace wa wani mutumi mazakuta

- Wasu matasa sun hadawa wani dan karamin wada jini da majina a garin Enugu

- Matasan sun dauki wannan hukunci a hannunsu ne bayan sun zargi wadan da sacewa wani mutumi mazakuta

- Mutumin ya bayyana cewa wadan ya sace mishi mazakutar ne bayan sun hada hannu sun gaisa

Tirkashi, masu fushi da fushin wani, sun huce haushinsu akan wani dan karamin wada wanda aka bayyana sunanshi da Anayo, bayan wani mutumi yayi ihun cewa an debe masa mazakutarsa a yankin Obiagu dake garin Ogui cikin jihar Enugu.

'Yan sanda ne suka kwato Anayo dakyar bayan matasan sun hada masa jini da majina a ranar Asabar dinnan da ta gabata 14 ga watan Satumba, bayan sun zarge shi da daukewa wani mutumi mazakuta yayin da suka hada hannu suka gaisa dashi.

KU KARAANTA: Tirkashi: Iya wadanda ke da digiri a dakikanci da rashin hankali ne kawai zasu bar PDP su koma APC - Dino Melaye

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Enugu, Ebere Amaraizu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutumin da ya bayyana cewa an sace masa mazakutar ya bayyana sunan shi da Sunday Ebubechukwu. Sannan ya bayyana cewa yanzu haka 'yan sanda suna nan suna bincike akan lamarin.

Ana cigaba da samun karin laifuffuka kala-kala a cikin Najeriya, wadanda suka hada da kashe-kashe, garkuwa da mutane, fyade da dai sauransu duk kuwa da irin kokarin da hukumomin tsaro keyi amma har yanzu lamarin yaki cin tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel