Babu matsala mun hakura - Martanin Buhari ga tawagar wakilan shugaban kasar Afirka ta kudu

Babu matsala mun hakura - Martanin Buhari ga tawagar wakilan shugaban kasar Afirka ta kudu

A ranar Litinin, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hakurin shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, kan hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya a kasarsa.

Shugaba Buhari, wanda ya siffanta wannan hare-hare a matsayin abin takaici ya ce duk da hakan, za'a cigaba da karfafa alaka tsakanin kasashen guda biyu.

Buhari ya tunawa wakilan shugaban kasan irin namijin gudunmuwar da Najeriya ta baiwa kasar Afirka ta kudu saboda yawancin matasan kasar sun jahilci tarihi.

Shugaba Buhari ya gana da wakilan shugaban kasar Afrika ta kudu na musamman Dr. K. Mbatta da Jeff Radebe a birnin tarayya Abuja.

Wadanda suka halarci taron sune ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama da jakadan Najeriya zuwa Afirka ta kudu, Kabiru Bala.

A jiya, Shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya roki gwamnatin Najeriya ta yi masa afuwa kan hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya dake zaune a kasarsa.

Wakilan shugaban kasan na musamman daga kasar Afirka ta kudu sun mika kokon barar hakurin al'ummar kasarsu ga shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Aso Villa Abuja.

Ramaphosa ya aiko wakilai uku na musamman zuwa kasashen Afrika bakwai, wanda ya hada da Najeriya domin neman afuwar kasashen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel