Gwamnatin Kwara ta ki karbar kayayyakin karatu da Saraki ya bawa makarantun jihar

Gwamnatin Kwara ta ki karbar kayayyakin karatu da Saraki ya bawa makarantun jihar

- Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana dalilin da yasa ta ki karbar kayan karatun da Saraki ya bawa wasu makarantu a jihar

- Saraki ya bayyana niyyarsa na bayar da gudunmawar wasu kayayyakin karatu ga wasu makarantu a jihar

- Sai dai gwamnatin jihar ta yi watsi da gudunmawar na Saraki saboda zai saka hotonsa a kan kayayakin da za a rabawa makarantun

Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana dalilin da yasa ta ki karbar kayayyakin karatu da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bawa wasu makarantu a jihar.

Legit.ng ta ruwaito cewa sanya hotonsa da sunansa kan kayayyakin da zai bawa makarantun ne yasa ta ki karbar kyautan duba da cewa kudin ayyukan.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa sakataren yada labarai na ma'aikatar ilimi da cigaban al'umma, Yakub Aliagan ya ce ma'aikatar ba ta san cewa Saraki zai bawa makarantu kayayyakin ba tun farko cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin 16 ga watan Satumba.

DUBA WANNAN: Mata sun lakada wa mijinsu duka saboda zai kara mata ta uku

"Gwamnatin jihar ba ta masaniya cewa za a rabawa makarantu kayayyakin rubuto da karatun tun farko. Abinda ya dace shine a aike da kayayakin zuwa ma'aikatar ilimi wadda aka dora wa alhakakin tantance inganci da cancanta kayayakin kafin ta bayar da izinin rabar da su.

"Rashin yin hakan sabawa doka ne. Baya ga hakan ba dai-dai bane mutum ya sanya hotonsa na wasu tamburarsa kan kayayakin karatu da za a rabawa dalibai a makarantun gwamnati.

"An ce kayayakin an siyo su ne da kudin gwamnatin tarayya a matsayin ayyukan mazabu," inji shi.

Aligan ya ce Gwamna Abdulrahmaza Abdulrazak ne jihar ya ki amincewa a saka hotonsa kan wasu kayayakin karatu da za a rabawa makarantun gwamnati a jihar.

Ya ce ma'aikatan ilimin ta tuntubi gwamnan domin a samar da kayayyakin karatu masu yawa da za a saka hotonsa a kai a rabawa dalibai idan sun dawo makaranta amma ya ki amincewa da hakan.

"Ya ki amincewa da hakan ne saboda dai dace mutum ya saka hotonsa a kan aikin da ya yi da kudin gwamnati ba. Duba da hakan, mahukunta makarantar sunyi dai-dai da suka ki karbar kayayyakin saboda ma'aikatar ilimi ba ta san da su ba.

"Domin shi ilimi ba a sa siyasa a cikinsa musamman a makarantun firmare na yara kanana. Tunda da kudin gwamnati aka siyo kayan, muna ba ofishin Sanata Saraki shawara su koma ma'aikatan ilimi bayan sun cire hotunan ko tambarin siyasa da aka saka a kayayyakin," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel