Tirkashi: Soja ya hallaka dan sanda har lahira

Tirkashi: Soja ya hallaka dan sanda har lahira

- Hukumar 'yan sandan jihar Cross River ta cafke wani soja da laifin kisan sifetan Dan sanda

- Sojan mai mukamin kofur ya kashe Dan sandan ne yayin da Dan sandan ya tsare motarsu don bincike

- Majiyarmu tace daga musu abin ya fara har ya kai ga fada tsakaninsu

'Yan sanda sun tsare wani soja mai mukamin kofur mai suna Femi Awotayo, sakamakon zarginsa da ake da kashe wani sifetan Dan sanda mai suna Christopher Achong, a jihar Cross River.

An kama Awotayo mai aikin musamman da runduna ta 707 a jihar Benue, tare da wasu mutane hudu bayan aukuwar lamarin.

Jami'ar hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo, ta tabbatar da kamen ga wakilin jaridar Punch a ranar Litinin.

KU KARANTA: Ko kunsan dalilin kama mawaki Naziru M. Ahmad?

"Mun kama sojan tare da mutane hudu. Suna sashin binciken manyan laifuka na jihar nan don amsa tambayoyin bayan hakan zamu mikasu ga kotu," inji ta.

An gano cewa lamarin ya aiki ne a Anyikang a karamar hukumar Bekwara da ke jihar Cross River, inda Achong da ke jagorantar rundunar sintiri ya tsayar da motar haya don bincike akan babban titin Ogoja zuwa Katsina Ala.

Motar mai dauke da fasinjoji zuwa Calabar ta tsaya don bincike.

Majiya daga Bekwara tace musu ya barke tsakanin sojan da sifetan wanda hakan ya jawo hargitsi tsakaninsu inda aka kwashi sifetan zuwa babban asibitin Bekwara don agajin gaggawa. Jim kadan dai sifetan 'yan sandan yace ga garinku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel