Gwamna Umahi zai nada mutane 800 a matsayin masu bashi shawara

Gwamna Umahi zai nada mutane 800 a matsayin masu bashi shawara

Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi ya kammala shirin sake nada wasu sabbin mashawarta guda 800 da zasu taimaka masa a gwamnatinsa, baya ga wasu hadimai guda 4,000 daya rantsar a kwanakin baya, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Umahi ya bayyana haka ne a ranar Litinin a garin Abakaliki yayin da yake ganawa da kwamishinoninsa, yan majalisun dokokin jahar, shuwagabannin kananan hukumomi, masu rike da mukaman siysa da kuma masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA: Buhari zai kammala gyarar wutar Najeriya kafin karshen mulkinsa – Minista

Gwamnan yace: “Zamu nada sabbin hadimai guda 800, kuma daga yanzu ba ni zan dinga zabo su ba, shuwagabanni a matakin mazaba ne zasu zabosu, don haka za mu nada mashawarta guda 3 daga kowanne mazaba, masu ruwa da tsaki zasu zabo mutane biyu, yayin da shuwagabannin PDP zasu zabo mutum 1.

“Mashawarta masu zartarwa zasu samu albashin N150,000, hadimai zasu samu albashin N120,000, albashin kananan mashawarta kuma N100,000, manufarmu ita ce mu kara yawan mutane a gwamnati tare da basu kwarin gwiwar bayar da gudunmuwa. Duk wanda muka nada yana da aikinsa, akalla zamu bashi eka guda na gona domin ya dinga nomata.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Ministan wutar lantarki, Injiniya Mamman Saleh dan mutane Taraba ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tabbatar da ingantaccen wutar lantarki wanda babu daukewa a Najeriya kafin wa’adin mulkinsa ya kare.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da ya kai ziyarar gani da ido zuwa wasu tashoshin wutar lantarki guda biyu dake unguwannin Mando da Kudenda a garin Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel