UNGA: Tijjani Bande ya canji María Fernanda Espinosa Garcés

UNGA: Tijjani Bande ya canji María Fernanda Espinosa Garcés

- Wakilan Najeriya sun taya Tijjani Bande murnar zama Shugaban UNGA

- Farfesan Najeryar ya karbi aikin Misis María Fernanda Espinosa Garcés

- An yi bikin bada sandar aikin ne a Garin New York a farkon makon nan

A jiya Litinin, 16 ga Watan Satumba, 2019 ne aka yi bikin nadin Ambasada Tijjani Mohammed Bande a matsayin sabon shugaban babban zauren nan na UNGA na majalisar dinkin Duniya.

Tijjani Mohammed Bande ya karbi sandar iko daga hannun Misis María Fernanda Espinosa Garcés wanda wa’adin ta ya cika. Wasu ‘Yan Najeriya sun halarci bikin domin taya na su murna.

An ga hotunan sabon shugaban zauren na UNGA tare da Wakilan da gwamnatin Najeriya ta aiko. Daga cikinsu akwai Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Malam Garba Shehu.

KU KARANTA: Buhari ya tura manyan mutane 4 su wakilci Najeriya wajen bikin UNGA

Haka zalika an ga Ambasada Tijjani Bande tare da ‘yar uwarsa mutumiyar Najeriya, Amina J. Mohammed wanda ita ce ta biyu a majalisar dinkin Duniya mai kujerar mataimakiyar Sakatare.

Babbar Wakiliyar kungiyar kasashen Afrika na AU a majalisar dinkin Duniya, Fatima Kyari Mohammed ta halarci wannan biki da aka yi a New York domin ganin nadin Tijjani Bande.

Bayan Tijjani Bande ya karbi sanda daga hannun María Fernanda Espinosa Garcés, ya yi jawabi a gaban zauren inda Sakataren majalisar ta UN, António Guterres, yake zaune tare da wasu manya.

An yi wannan biki ne a babban Garin New York na kasar Amurka inda Hedikwatar majalisar dinkin Duniyar ta ke. Buhari Sallau ne ya dauki wannan hotuna da Sunday Aghaeze ya dauka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel