Sarki Sanusi ya yabawa Buhari game da nadin sabon kwamitin tattalin arziki

Sarki Sanusi ya yabawa Buhari game da nadin sabon kwamitin tattalin arziki

Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi Lamido II ya yabawa Shugaba Muhammadu Buhari na zakulo jajirtattu kuma masu kwarewa ta gaske a matsayin ‘yan cikin sabon kwamitin masu ba shi shawara game da tattalin arziki.

A ranar Litinin 16 ga watan Satumba ne Shugaban kasan ya nada sabon kwamitin da zai taimaka masa da shawarwari game da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA:Najeriya ta samu cigaba a bangaren noma – Bagudu

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da kwamitin, Sarkin Kano kuma tsohon Shugaban babban bankin Najeriya wato CBN ya ce shugaban kasan yayi daidai na zaben wannan mutane.

Sarkin ya ce wannan kwamitin zai matukar taimakawa Shugaban kasan a kan yin gyara tare da bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar ba shi shawarwari masu inganci.

Sarkin ya ce: “A nawa ra’ayin wannan shi ne abu mafi muhimmanci da Shugaban kasa ya soma yi a wa’adinsa na biyu. Ko shakka babu yayi zaben mutane masu hazaka da sanin akan abinda ya shafi tattalin arziki.

“A cikin wannan kwamitin kwararrune daga bangarori daban-daban na tattalin arziki Shugaban kasan ya zabo. Ba zan iya ce maku ga wasu mutanen da suka dara wadanda shugaban kasan ya zaba domin ba shi shawara game da tattalin arziki a yanzu ba.

“Shugaban kasa ya cancanci a yaba masa bisa wannan namijin aiki da yayi na zaben kwararru a fagen sanin tattalin arziki domin kasacewa masu ba shi shawarwari. Abinda kawai muke tsammani daga gare su yanzu shi ne gudanar da aikin da rataya a bisa kawunansu. Hakika ina cike da farin ciki a yau saboda nadin wannan kwamitin tattalin arziki.” Inji Sarki Sanusi.

https://leadership.ng/2019/09/17/emir-sanusi-commends-pmb-over-new-economic-team/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel