An kori wani jami'in dan sanda da aka kama da laifin sata

An kori wani jami'in dan sanda da aka kama da laifin sata

An kori wani jami'in dan sanda, Abdullahi Yusuf da ke aiki da rundunar 'yan sanda reshen jihar Jigawa saboda samunsa da satar talabijin da takalma.

Dan sanda da aka kora an ce mahaifinsa tsohon dan sanda ne da ya yi murabus daga aiki.

Kafar yadda labarai na Linda Ikeji's Blog ya ruwaito cewa Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Bala Senchi ya tabbatar da korar dan sandan mai mukamin constable da aka ce ya dade yana satar.

Mista Senchi ya ce, "Ana sa ran dan sanda ya kasance mutum mai da'a da halaye masu kyau shi yasa aka danka amanar rayuka da dukiyoyin al'umma a hannunsu. Rundunar 'yan sanda ba za ta kyale wani jami'i ya lalata sunan ta ba."

Rahotanni sun bayyana cewa Yusuf ta sace talabijin ne mallakar wani jami'in dan sandan makonni biyu da fitowarsa daga hannun sashin binciken manyan laifuka wato CID saboda wani satar da ya yi a baya.

DUBA WANNAN: Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

A yayin da ya ke bayyana yadda aka kama wanda ake zargin, wani mazaunin Unguwar Sarki a garin Dutse mai suna Muktar Yunusa ya ce korarren dan sandan ya masa kutse cikin gida ta hanyar amfani da mukulai biyar da rana tsaka.

Mista Yunusa ya ce, "Lokacin da ya fito daga gida na dauke da kayan satan da suka hada da talabijin, remot kontrol da takalma, na tambaye shi inda za shi da kayayakin sai ya nuna min kamar ya san mai gidan ba tare da ya san gida na bane.

"Daga bisani na kira wasu makwabta na inda muka kama shi muka tafi da shi ofishin 'yan sanda."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel